IQNA

Ministan Shari’a Na Kasar Masar Yana Karanta Kur’ani da Kure

23:55 - March 25, 2016
Lambar Labari: 3480262
Bangaren kasa da kasa, sabon ministan shari’a na kasar Masar ya karanta kur’ani mai tsarki da kurakurai masu muni.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misr yaum cewa, Muhammad Husam abdulrahim ya karanta kur’ani mai tsarkia cikin kure.

Tarihin yada wannan bidiyo shi ne a cikin watan Yunin shekara ta 2015 tare da halartar shugaban kasar Abdulfattah Sisi.

Sabon ministan shari’ar na kasar masar ya karanta wannan aya nea cikin wani matani da yake karantawa a wani taro , inda ya karnat abin da k erubuce a cikin kure ba tare da ya san abin da yake karantawa.

Ya karanta aya ta 227 a cikin surat Shu’ara inda ya karanta lafazin wadanda a matsayin wanda wato mai maimakin jam’I sais a mayar da shi mufradi. Kamar haka nan kuam acikin aya ta 8 an cikin surat Al Imran yay i wani bababn kuren, wanda kuma ya zo nea acikin aya wadda take dauke da addu’a da ake yawan karanta atsakanin dukaknin al’ummomin musulmi wadda ta zama jiki.

Haka nan kumawajen rufe karatun nasa yay i wani babban kuran da ke nuna cewa bas hi da wata masaniya kan kur’ani mai tsarki, wanda kuma shi ne ya zama babban alkali a daya daga cikin manyan kasashen musulmi na duniya.

3484465

captcha