IQNA

Malaman Jami'oi Sun BukaCi Azhar Ta Cre Ayoyin Jihadi Daga Manhajarta

22:38 - July 03, 2016
Lambar Labari: 3480576
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin malaman jami'oi a kasar Masar sun bakaci babbar cibiyar addini ta kasar Azhar, da ta cire wasu daga cikin ayoyin jihadi daga manhajarta ta koyarwa, domin kauce wa yin amfani da hakan wajen ayyukan ta'addanci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaum Sabi wadda ta buga a shafinta na yanar gizo a yau cewa, wasu fitattun malaman jami'a na kasar sun bukaci Azahar da ta cire ayoyin da ke yin kira zuwa ga jihadi ne, domin 'yan ta'adda suna daukar wadannan ayoyin ne kawai daga cikin kur'ani domin baka kansu hujja wajen aikata ta'addanci da sunan jihadi, suka a maimakon haka a mayar da hakankali a kan ayoyin da suke kira zuwa ga zaman lafiya da rahama da tausayia tsakanin 'yan adam.


Shi ma a nasa bangaren ministan harkokin al'adu na kasar ta Masar Jabir Asfur ya nuna goyon bayansa ga wannan kira na malaman jami'oin kasar ta Masar ga cibiyar Azahar, inda a cewarsa hakan baya yana nufin rashin amincewa da ayoytin ba ne, illa dai yin amfani da hikima wajen kauce wa duk wani aiki na bata sunan muslunci tare da fakewa da ayoyin kur'ani.

Tun kafin wanann lokacin dai gwamnatin kasar Morocco ta sanar da cire ayoyin da suke yin kira zuwa ga jihadia cikin manhajar koyarwa amakarantun kasar, da suna kauce wa yin amfani da hakan wajen aikata ta'addanci da sunan jihadi.

3512319

captcha