IQNA

Tarayyar Turai Ta Yi Allawadai Da Masarautar Al-Khalifah

21:41 - July 09, 2016
Lambar Labari: 3480594
Bangaren kasa da kasa, majalisar kungiyar tarayyar turai ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da keta hurumin bil adama da masarautar Al Khalifa ke yi a Bahrain.
Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Mana Post cewa, majalisar kungiyar tarayyar turai ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da keta hurumin bil adama da masarautar Al Khalifa ke yi a Bahrain saboda dalilai na siyasa.

Kashi tamanin da daya na dukkanin mambobin majalisar kungiyar tarayyar turai sun kada kuri'ar amincewa da wani daftarin kudiri, wanda ya yi Allawadai da kakkausar murya kan cin zarafin 'yan adam da kama karya da masarautar Bahrain ke yi kan al'ummar kasar.

An dai gabatar da wannan daftarin kudirin ne bayan hardahada rahotanni da manyan kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suka yi kan cin zarafin dan adam da keta huruminsa da gwamnatin Bahrain ke yi saboda dalilai na siyasa da bangaranci na mazhaba, musamman ma mabiya mazhabar shi'a wadanda su ne fiye da kashi tamanin da biyar na al'ummar kasar ta Bahrain.

Kungiyoyin sun yi ishara da matakan baya-bayan na da masarautar kasar ta dauka, na daure babban sakaren jam'iyyar siyasa mafi girama a kasar ta Al-wifaq Sheikh Ali Salman, duk kuwa da cewa dama tsarin kasar bai yarda da mulkin dimukradiyya ba, sai kuma batun kama shugaban cibiyar kare hakkin bil adama a kasar Nabi Rajab, gami da janye izin zama dan kasa daga babban malamin addini na kasar Sheikh Isa Kasim.

Wannan mataki na majalisar kungiyar tarayyar da ke yin Allawadai da masarautar Bahrain da ya zo ne a matsayin ba zata ga masarautar Bahrain, inda take ganin hakan a matsayin wani mataki ne juya mata baya daga kasashen turai da take dasawa da su, kuma suke mara mata baya.

3513620

captcha