Obama yana mayar da martani ne a fakaice a cikin bayanin nasa a kan Donald Trump dan takarar shugabancin Amurka a karkashin inuwar jam'iyyar Republican, wanda ya bayyana adawarsa karbar musulmi masu yin gudun hijira zuwa Amurka, inda yake bayyana hakan a matsayin bababn hadari na karuwar ta'addanci a kasar.
Gwamnatin barck Obama dai ta karbi dubban musulmi 'yan gudun hijira daga kasashe daban-daban, da hakan ya hada da dubban 'yan kasar Syria, da suka tsere wa yakin da aka haifar a kasarsu, lamarin ke ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga masu kyamar musulmi, musamamn ma magoya bayan Donald Trump na jam'iyyar Republican.