IQNA

Daurin Watanni 8 A Gidan Kaso Kan Masu Wulakanta Masallaci A Landan

16:48 - November 03, 2016
Lambar Labari: 3480905
Bangaren kasa da kasa, wata kotu a Landan ta yanke hukuncin daurin watanni 8 a wasu mutane biyu, saboda jefa naman alade da suka yia kan masallacin Rahman da ke birnin.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Thesun cewa, Motoz Poiluksuki dan shekaru 22 da haihuwa da kuma Pioter Zak zakuky dan shekaru 28 an yanke musu hukuncin daurin watanni takwas a gidan kaso.

Kotun da Landan ta yanke hukuncin daurin watanni 8 ne a kan mutanen biyu, saboda jefa naman alade da suka yia kan wani masallaci a lokacin da musulmi suke salla a cikinsa, inda alkalin ya ce abin da suka yi nuna kiyayya ne ga wasu 'yan kasa saboda addininsu da kuma akidarsu, wanda yin hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Kyamar musulmi ta kasua kasar ta Birtaniya da ma wasu kasashen turai ne sakamakon hare-haren bayan na da aka kai a birnin Parsi da wasu biranan kasashen turai, wanda yan ta’adda ma su kiran kansu musulmi suke kaiwa.

Kungiyoyin kare hakkin bil adama da dama suna nuna damuwa dangane da yadda kyamar musulmi ke karuwa a nahiyar, duk kuwa da cewa ayyukan ta’addancin da ake yi da dama suna shafar msuulmin ne hatta a cikin kasashne turai.

3542859


captcha