IQNA

Masu Daukar Hotu A UAE Sun Mayar Da Hankali Ga Karatun Hananah

22:47 - November 05, 2016
Lambar Labari: 3480910
Bangaren kasa da kasa, Hananah Khalfi mai wakiltar Iran a gasar karatun kur’ani ta mata a kasar hadaddiyar daular larabawa ta wuce matakin farko na shiga gasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, Musatafa Khalfi mahaifin Hananah a zanatawarsa da iqna ya bayyana cewa, ta amsa dukkanin tambayoyin da aka yi mata wanda ya bata damar zama daya daga cikin wadanda za su shiga gasr.

Ya ci gaba da cewa duk da cewa wannan shi ne karo na farko da ake gudanar da wannan gasa, amma daga yadda ta amsa tambayoyin ya nuna cewa tana kyakkayawan shiri na yin gasar.

Haka nan kuma dangane da yadda ta zama ta ja hankali masu daukar hotuna a gasar tun daga tashin farko, ya bayyana cewa wata kila hakan bai rasa nasaba da karancin shekarunta idan aka kwatanta da sauran mata da suka zo daga kasashen duniya daban-daban, da kuma yadda ta amsa dukkanin tambayoyin da aka yi mata ba tare da wani kure ba.

Wanna gasa ta kasa da kasa dai za ta gudane nea babban ginin cibiyar yada al’adun muslunci da ke birnin Dubai, wanda kuma bisa ga al’ada ana gudanar da tarukan gasar kur’ani ta kasa da kasa a wannan wuri tsawon shekaru.

Akwai alkalan gasar su 6 da aka sanar da sunayensu wadanda dukkaninsu sun hallara, kuma tuni suka fara gudanar da aikinsu, wadanda sun fito ne daga kasashen Saudiyyah, Masar, Jordan, UAE, Algeria, da kuma Iraki.

3543417


captcha