IQNA

Zanga-Zangar Daliban Jami'a Musulmi Kan Kin Amincewa Da Kyamar Musulmi A New York

20:37 - November 12, 2016
Lambar Labari: 3480933
Bangaren kasa da kasa, wasu daga daliban jami'a musulmi a birnin New York sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da kyamar musulmi.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na NYULocal cewa, wani daya daga cikin musulmi dalibai ya shiga masallaci da nufin gudanar da salla sai ya ga hoton Trump.

Bayan kammala salla daliban sun fito kan titi suna jerin gwano suna yin kira ga sabon shugaban kasar da sauran masu akidar kymar musulmi a kasar da su sake yin nazari.

Daliban sun bukaci Trump da ya zama shuga na dukkanin Amurkawa da suka hada da muslmi da ma wadanda ba msuulmi ba, a kan haka dole ne ya yi adalci a matsayinsa na zababben shugaban Amurka.

Bayan lashe shugaban kasar da ya yi Trump ya yi kalamai masu ban mamaki, inda y ace zai mulki ba tare da nuna kyama ga wani bangare ba saboda banbancin akida ko addini ko launin fata, zai yi aiki tare da dukkanin al'ummar Amurka baki daya.

Tun bayan sanar da lashen shugaban kasa da Trum ya yi musulmin kasar Amurka suna cikin halin damuwa, musamman saboda irin kalaman batuncin da ya yi ta yi a kansu a lokacin yakin neman zabe.

3545293


captcha