Bisa ga al’ada duk bayan makonni hudu watan ya matso kusa da kasa, amma wannan ya sha banban matuka, domin girmansa ba irin wanda aka saba gani ba ne, domin kuwa matso kusa da kasa fiye da abin da aka sanbi bisa al’ada.
Wasu masana suna cewa hakan na faruwa ne sau daya a cikin shekaru saba’in, kumaba zai sake faruwa ba sai bayan wasu shekaru saba’in a nan gaba.
A lokacin da aka ga wata ya yi irin wannan shi ne ake kiransa giwan wata, ko kuma (supermoon) a turance.