A bangare guda, 'yan uwa musulmi almajiran shekh Ibrahim Yakubu Elzakzaky dake birnin Abuja sun gudanar da zanga-zanga a jiya Laraba domin nuna bacin rai da adawa kan kisan gillar da jami'an tsaron jihar Kano suka yiwa 'yan uwansu a yayin da suka tattaki na zagayowar ranar arabi'in din Imam Husain ranar Litinin din da ta gabata.
Mahalarta zanga-zangar sun tabbatar da cewa Jami'an tsaron Kanon sun hallaka 'yan uwa sama da dari tare kuma da da yin awan gaba da gawawwakinsu.a yayin da suka isa cibiyar kare hakin bil-adama ta kasar sun bukaci kungiyar da ta shaidawa Shugaban kasar cewa su ma 'yan kasa ne,dole a kare musu hakin su kamar ko wani dan kasa, bai dace ba a dinga kai musu hari a yayin da suke gudanar da addininsu.