IQNA

Adadin Masu Ziyarar Arbaeen A Karbala Yana Karuwa

22:50 - November 19, 2016
Lambar Labari: 3480953
Bangaren kasa da kasa, adadin masu gudanar da ziyarar arbaeen na Imam Hussain (AS) a Karbala yana karuwa.
Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alfurat News cewa, Nasif Alkhitabi shugaban majalisar lardin Karbala ya bayyana cewa, adadini mutane da suka isa Karbala ya zuwa yanzu ya kai mutum miliyan ashirin.

Ya ci gaba da cewa tun daga lokacin da aka fara gudanar da tarukan na arbaeen daga makon da ya gabata, ya zuwa masu ziyara daga kasashen ketare miliyan uku da rabi ne suka isa birnin karbala, yayin da kuma fiye da Irakawa miliyan shida daga sassa na kasar suka isa birnin domin gudanar da tarukan na ziyarar arbaeen.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, za a ci gaba da gudanar da ayyukan ziyarar ta arbaeen daga nan har zwa ranar Litinin, a kan ba zai yiwu a iya bayar da hakikanin alkalumma na krashe ba dangane da adadin masu ziyarar na ciki da wajen kasar Iraki ba.

Ya ce a halin yanzu za a iya cewa adadin masu shiga da fita birnin na Karbala ksan daya ne, domin a halin yanzu mutanen da suka yi ziyara suna fita ne, saboda babu wurin zama, garin ya gama cika makil da mutane.

3547262


captcha