IQNA

Jagoran Juyin Juya Hali:

Amurka Dai Ita Ce Amurka, Babu Wani Banbanci A Wurinmu Kan Sakamakon Zabe

23:50 - November 21, 2016
Lambar Labari: 3480959
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a wata ganawa da yayi da dubun dubatan mutanen garin Esfahan, ya bayyana cewa a wurin Iran babu wani banbanci kan wanda ya lashe zabe a Amurka.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yanar gizo na jagora cewa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, a wata ganawa da yayi a yau Laraba (16-11-2016) da dubun dubatan mutanen garin Esfahan, ya bayyana cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta yi wani hukunci dangane da zaben shugaban kasar Amurka ba don kuwa tsawon shekaru ba abin da suke gani tattare da wadannan jam'iyyu biyu face kiyayya inda ya ce: A halin yanzu babban abin da kasar Iran take bukata musamman daga wajen masana da jami'an gwamnati shi ne 'basira cikin siyasa da kuma rashin gafala daga makircin makiya', 'kiyayi ruhi da mahangar juyin juya hali', 'aiki tukuru a fagen tattalin arziki na dogaro da kai', 'ci gaba ba kamu hannun yaro a fagen ilimi', 'hadin kai da aiki tare na kasa' da kuma 'kiyaye irin karfi na cikin gida da ake da shi'.

A yayin wannan ganawar wacce aka gudanar da ita don tunawa da yunkurin mutanen garin Esfahan a wajen jana'izar shahidai 370 a shekarar 1361 inda ya bayyana cewar daya daga cikin siffofin da mutanen Isfahan suka kebanta da su shi ne ruhin neman shahada da kuma tsayin daka. Haka nan kuma yayin da yake jaddada wajibcin fahimtar makirce-makircen makiya a koda yaushe da kuma rashin mika musu kai, Jagoran ya ce: Tsayin daka bisa tushen juyin juya halin Musulunci daya ne daga cikin muhimman bukatun da ake da su a yau din nan. Tushen koyarwar juyin juya halin Musulunci kuwa su ne dai wadannan abubuwan da marigayi Imam Khumaini (r.a) ya bayyana da kuma abubuwan da suke cikin wasiyyar da ya bari.

Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar hanya guda kawai ta magance matsalar kasar Iran da kuma cike gibin da aka fuskanta tsawon shekarun da suka gaba da kuma tabbatar da daukaka da ci gaba na duniya da lahira shi ne tsayin daka wajen ci gaba da riko da koyarwar juyin juya halin Musulunci, inda ya ce: A aikace ma wajibi ne a ci gaba da karfafa irin karfi na cikin gida da ake da shi musamman a bangaren tattalin arziki.

Nuna basira ta siyasa ma dai na daga cikin bukatun da ake da shi a kasar Iran musamman a tsakanin masana da jami'an kasar inji Jagoran juyin juya halin Musulunci inda ya ke cewa: Rashin basirar shi ne ke sanya mutum ya mika kai ga wani abin da a hakikanin gaskiya ba shi da wani abin jan hankali a tattare da shi, kamar yadda Amurka ta janyo hankulan wasu, alhali kuwa wannan jan hankalin na karya ne.

Har ila yau kuma a cikin jawabin nasa Jagoran juyin juya halin Musulunci yayi karin haske dangane da abubuwan da aka gabatar dangane da matsaloli da kuma hakikanin al'ummar Amurka a yayin yakin neman zaben shugabancin kasar inda ya ce: Mutumin da aka zaba a matsayin shugaban kasar Amurka, a yayin yakin neman zabe ya bayyana cewar idan da a ce kudaden da muka kashe tsawon shekarun nan da an kashe su ne a cikin gidan Amurka da kuwa mun sake gida kasar har sau biyu; shin mutanen da Amurkan take burges su sun fahimci ma'anar wannan magana kuwa?

Haka nan kuma yayin da yake magana kan abubuwan da aka gabatar a yayin yakin neman zaben da ke nuni da talauci da matsaloli masu yawan gaske da Amurka take fuskanta, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: (Gwamnatocin) Amurka tsawon shekarun baya-bayan nan sun kashe kudaden al'ummar kasar wajen kaddamar da yakukuwa wadanda sakamakonsu shi ne kashe dubun dubatan fararen hula da ruguza kasashen Afghanistan, Iraki, Libiya, Siriya da Yemen.

Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar abubuwan da aka ta fadi yayin yakin neman zaben Amurka su ne dai abubuwan a tsawon shekarun nan ake ta fadinsu amma wasu sun yi yarda su fahimci abin da ake cewa. Jagoran ya ce: Ma'anar basira ita ce fahimtar da wa ake fada, sannan shi kuma yaya yake kallonka. Idan kuwa ka rufe idanuwanka nan take zai cutar da kai.

Don haka yayin da yake bayanin cewa irin wannan basira ita ce fatan da ake da shi daga wajen masana na siyasa da ma wadanda ba na siyasa ba, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Abu mai faranta rai shi ne cewa mutanen gari suna da irin wannan basirar, to amma abin mamakin shi ne cewa wasu daga cikin masana sun rasa irin wannan basirar.

Haka nan kuma yayin da yake magana kan sakamakon zaben shugabancin Amurka, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Mu dai babu wani hukunci da za mu yanke dangane da wannan zaben, don kuwa Amurka dai ita ce dai wancan Amurkan. Tsawon wadannan shekaru 37 da suka gabata babu wani alheri da muka gani daga wajen wadannan jam'iyyu guda biyu a lokacin mulkinsu, a kullum sharrinsu ne kawai yake samun al'ummar Iran.

Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Sabanin wasu mutane a duniya da suka kasance cikin bakin ciki ko kuma farin ciki sakamakon fitar da sakamakon zaben Amurka, to mu dai ba ma cikin bakin ciki haka nan ba ma cikin farin ciki, don kuwa babu wani bambanci a wajenmu, kuma ba ma cikin wata damuwa. Cikin yardar Allah muna cikin shirin tinkarar duk wani abin da zai faru.

Jagoran ya ci gaba da cewa: Lamarin da ya kamata mu fi ba shi muhimmanci a halin yanzu shi ne hanyar da za mu magance matsalolin da kasar nan take fuskanta a halin yanzu da kuma nan gaba. Hanya guda ta cimma hakan kuwa ita ce kiyayewa da kuma karfafa irin hadin kai na cikin gida da ake da shi.

3546535


captcha