IQNA

Dan Wasan Fina-Finan Amurka: Kiran Sallah Na Cikin Sautuka Mafi Kyau A Duniya

21:49 - November 24, 2016
Lambar Labari: 3480969
Bangaren kasa da kasa, Morgan Freeman dan wasan fina-finai a kasar Amurka ya bayyana cewa,kiran salla na daga cikin sautuka mafi kyaua duniya.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Press TV cewa, Morgan Freeman yana hada wani shiri ne a tashar National Geographic a lokacin da yake amsa tambaya kan shirinsa nasa wanda yake da alaka da Imani da ubangiji, sai ya bayyana cewa kiran salla na daga cikin sautuka mafi kyau a duniya.

Ya ce ya yi bincike matuka dangane da lamrurran da suka shafi addinai, amma dangane da muslunci ya ga abubuwa na ban mamaki, daga ciki kuwa har da kiran sallah da musulmi suke yi a masallatai kafin fara salla, wanda acewarsa yana daga cikin sautuka mafi dadi da tasiri ga dan adama a duniya.

Ya ce yana son ya san yadda masu kiran sallah suke koyon yinsa kafin su fara shin suna halartar wani aji na musamman ne kan hakan?

A ranar 3 ga watan Afirilun 2016 ne aka watsa shirinsa a karin farko, ya zuwa yanzu an watsa bangare 6 daga cikinsa a talabijin.

A cikin muharram na wannan shekarar ne ya halarci taron Ashura a birnin London na kasar Birtaniya, inda yake ganewa idanunsa abin da ake gudanarwa, domin hakan ya taimaka masa a shirinsa.

Ya karbi kyautuka da daman a fina-finai, da hakan ya hada da kyautar oska a cikin shekara ta 2005, sai kuma a cikin shekara ta 2012 ya karbi kyautar wani fim na Golden Club wanda ya samu karbuwa a tsakanin Amurkawa.

3548590


captcha