IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Sirar Manzon Allah (SAW) A Morocco

20:58 - November 25, 2016
Lambar Labari: 3480972
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da zaman taro na biyu na kasa da kasa kan tarihin manzon Allah (SAW) a birnin fas na kasar Morroco.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanbin dillancin labaran Ina cewa, wannan taro nana gudanar da shi ne bisa hadin gwiwa tsakanin cibiyar yada al’adu da kuma ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Morocco.

A wannan taro mai taken sirar manzon tsira Almustafa (SAW) malamai da masana da kuma yan jami’a suna gabatar da jawabai da laccoci, dangane da matsayin manzo da kuma gudunmawar da ya baiwa addini da kuma bil adama.

Abdullah Gazi ministan mai kula da harkokin addinia kasar Guinea Konacry ya bayyana gaban taron cewa, manzon Allah manzo ne na rahma ga dukaknin bil adama, shi ne manzo manzo da ya kawo zaman lafiya da fahimtar juna a tsakanin dukkanin addinai.

Ya kara da cewa sirar manzon Allah cike da darussa ga dukkanin yan dam, ta fuskar siyasa, zamantakewa tsarin tattalin arziki da kyawawan dabiu da dukkanin abin da mutum yake bukata na rayuwa akwai abin koyi daga rayuwar manzon Allah (SAW).

Muhammad Alruki shi ne shugaban jami’ar Alwarawiyyin, ya gabatar da tasa laccainda yake cewa, idan da dukkanin musulmi za su yi riko da koyarwar da manzo ya yi musu, da sun zama mafita ga dukkanin matsaloli na duniya, da kuma ba asamu wadanda za su fandare su rika yin ta’addanci da sunan muslnci ba.

Ya ce dogaro ga kur’ani da koyarwar manzo sune mafita ga dukkanin matsalolin da musulmi suke fuskanta a wannan zamani, kuma matkar za a koma ga koyarwar manzo to za a fahimci koyarwar kur’ani mai tsarki, kuma za azauna lafiya za arayu cikin sa’ada ta duniya da lahira.

3548680


captcha