Babbar manufar gudanar da wannan baje koli dai ita ce bayyana hakinanin koyarwa ta kur'ani mai tsarki, sabann irin yadda ake yada mummunar fusa dangane da addinin muslunci da kuma kur'ani mai tsarki.
Kasar dai tana daga cikin kasashen da musulmi kan yawaita yin hijia zuwa cikinta, amma daga bisani sakamakon bullar ayyukan masu akidar kafirta muuslmi da kuma ayyukan ta'addancin da suke gudanarwa da sunan muslunci, hakan ya bata sunan mulsunci matuka a wurin mutanen kasar Australia.
Wannan ne ya sanya masana daga cikin musulmi da suke zaune a kasar mikewa wajen ganin sun wayar da kan al'ummar kasar dangane da musulunci da kuma hakikanin koyarwarsa, da kuma banbancin muslunci na gaskiya da kuma 'yan ta'adda, kuma ga dukkanin alamu hakan yana yin tasiri.