IQNA

Tir Da Allawadai Da Mulkin Kama Karya A Bahrain

21:40 - November 26, 2016
Lambar Labari: 3480976
Bangaren kasa da kasa, al'ummar kasar Bahrain sun gudanar da wata gagarumar zanga-zanga yin Allawadai da salon mulkin kama karya na masautar Al khalifah a kan al'ummar kasar.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin Mehr cewa, Mehr ya bayar da rahoton cewa, a jiya dubban mutane ne suka gudanar da gangami a sassa daban-daban na kasar Bahrain, domin nuna rashin amincewarsu da mulkin kama karya a kansu.

Masu gangamin sun rika rera taken nuna rashin amincewarsu da hana al'ummar yankin Diraz gudanar da sallar Juma'a tsawon makonni ashirin da hudu a jere, kamar yadda kuma suka jaddada goyon bayansu ga babban malamin addinin muslunci na kasar Sheikh Isa Kasim, wanda masarautar kasar ta sanar da janye masa izinin zama dan kasa, saboda dalilai na siyasa da bangaranci na mazhaba.

Tun a cikin watan Yunin da ya gabata ne masarautar kasar Bahrain ta sanar da soke izinin zama dan kasa a kan Sheikh Isa Kasim, tare da yunkirin kama shi domin gurfanar da shi a kotu, amma hakan ya gagara, sakamakon matakan da al'ummar kasar suka dauka na ba shi kariya, da kuma bain da ka iya biyo baya akasar matukar mahukuntan kasar suka yi amfani da karfin domin kama shi.

Fiye da kashi 85% na mutanen kasar Bahrain dai mabiya mazhabar shi'a ne, yayin da mahukunatna kasar kuma mabiya akidar wahabiyanci ne, sauran al'ummar kasar kuma sun hada da 'yan sunnah, kiristoci da kuma 'yan darikar abadiyyah.

3549130


captcha