Kamfanin dillanicn labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ‘yan majalisar dokokin kasar Iran 191 ne suka fitar da bayani wanda suka sanya hannu a kansa dangane da kisan gillar da mahukuntan masarautar ‘ya’yan gidan Saud suka yi babban malamin addini Ayatollah Baqir Nimr a shekarar da ta gabata.
Babban abin da bayanin majalisar ya kunsa
Ya yi tir da kisan da mahukuntan Saudiyyar su ka yi wa malamin na shi'a mai gwagwarmaya na kasar Saudiyya, sannan kuma ta zargi kungiyoyin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa da yin fuska biyu wajen mu'amala da zuriyar ali-Sa'ud.
Bugu da kari bayani wanda majalisar ta fitar a yau talata da ita ce ranar da malamin ya cika shekara guda da yin shahada, ya ci gaba da cewa; kashe Sheikh Nimr da ali-Sa'ud su ka yi a daidai lokacin da yankin gabas ta tsakiya ya ke fama da matsalar ta'addanci da rashin tsaro, yana nuni ne da rashin tsari da hangen nesa na ali-Sa'ud.
A ranar sha biyar ga watan oktoba na dubu biyu d sha biyar ne wata kotu a kasar Saudiyya ta yanke hukuncin kisa akan shehin malamin, ta hanyar fille kanshi da takobi sannan kuma a rataye gangar jikinsa a fili inda mutane za su gani."
An kuwa zarar da hukuncin kisar a kanshi ne a ranar biyu ga watan janairu na shekara ta dubu biyu da sha shida.