IQNA

Kisan Kananan Yara Palastinawa Da Isra’ila Ke Yi Ya Karu A Shekarar Da Ta Gabata

23:57 - January 05, 2017
Lambar Labari: 3481105
Bangaren kasa da kasa, wani sabon rahoto yi ya yi nuni da karuwar kisan kananan yara Palastinawa da Haramtacciyar kasar Isra’ila ke yi s shekarar 2016.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga tashar Press TV cewa, cibiyar kare hakkokin kananan yara ta kasa da kasa ta fitar da sabon rahoton da ta harhada dangane da halin da kananan yara suke ciki a cikin yankunan Palastinawa da ke karkashin mamayar Isra’ila.

Rahoton ya ce a cikin shekarar da ta gabata Isra’ila ta kasha kananan yara Palastinawa 34 tare da jikkata wasu 83, ba tare da wadannan yaran sun aikata wani abu wanda suka cancanci kisa a kansa ba.

Babban daraktan kungiyar ya sheda wa tashar Press TV cewa, suna da kwararan dalilai da ke tabbatar da cewa, Isra’ila tana yin amfani da karfi a kan Palastinawa fararen hula, tare da kashe kananan yara da ba su aikata laifin komai ba, illa dai kawai laifinsu shi ne su Palastinawa ne.

Ya kara da cewa babban abin bakin ciki shi ne dukkanin laifukan yaki da Isra’ila take tafkawa a kan idon ‘yan jarida na kasa da kasa take aikata shi, kuma babu wanda ya isa ya ce da ita uffan, saboda manyan kasashen duniya musamman na turai daga cikinsu, su ne ke bata cikakkiyar kariya kan dukkanin abin da take iakatawa.

Abin tuni a nan dais hi ne, tun daga watan Oktoban shekarar 2015 ya zuwa yanzu, Isra’ila ta kasha Palastinawa fararen hula 244 a cikin yankunansu daban-daban da take mamaye da su.

3559972


captcha