IQNA

Wadanne Ayoyin Kur’ani Ne Aka Karanra A Lokacin Rantsar Da Trump

22:54 - January 22, 2017
Lambar Labari: 3481158
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Majid daya daga cikin manyan limaman musulmi na kasar Amurka, a lokacin da ake ci gaba da bukin ratsuwar Trump a wata majami’ar birnin Washington ya karanta ayoyin kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya bayar da rahoton cewa, tashar talabijin ta CNN ta ce an saba gudanar da irin wannan taro ne tun daga lokacin tsohon shugaban Amurka George Washington.

Muhammad Majid shi ne limamin masallacin Adams daya daga cikin manyan masallataa kasar Amurka da ke cikin jahar Virginia.

Majid ya yi nfin isar da wani sako na siyasa da zamantakewa zuwa ga sabon shugaban kasar ta Amurka, inda ya zabi wasu daga cikin ayoyin kur’ani mai tsarki da suke da alaka da sakon da sakon da yake son isarwa ga Trump da ma duk wani mai tunani irin nasa.

Da farko dai ya fara da aya ta 13 a cikin surat Hujrat, wadda take Magana a kan cewa Allah madaukakin sarki ya halici mutane maza da mata ya sanya su al’ummomi da kabilu domin su fahimci juna a cikin rayuwar ta duniya da kuma zamantakewarsu, amma a wurin Allah ma’aunin daukaka shi ne yafi jin tsoron Allah a rayuwar duniya.

Haka nan kuma malamin ya karanto aya ta 22 a cikin surat Rum, wadda take Magana a kan cewa Allah madaukakin sarki shi ne ya halicci sammai da kassai kuma a cikin wannanhalitta da yay i ta sammai da kassai da banbanta launukan mutane da harsunansu akwai aya mai girma ga masu ilimi da hankalta da idon basira.

Majid ya kasance daya daga cikin fitattun mutane 26 da aka gayyata zuwa ga wannan taro domin ya zama wakilin musulmi a wurin taron.

Rezwan Jaka shi ne babban darakta na masallacin Adams, ya bayyana cewa Majid ya zabi wadanna ayoyi ne domin ya isar da sakon addinin muslunci ga duniya, tare da tabbatar ma duniya cewa muslunci addinin zaman lafiya da fahimtar juna, musulunci addini ne da yake girmama dan adam ba tare da banbancin kabila ko launin fata ko harshe ko al’adu ba.

3565287


Trump


captcha