IQNA

Bankin Mulsunci Na Samun Karbuwa A Kasar Mauritania

23:14 - January 26, 2017
Lambar Labari: 3481171
Bangaren kasa da kasa, ayyukan bankin musulunci na ci gaba da bunkasa a kasar Mauritania.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran kasar Mauritania cewa, Abdulazizi Wuld Al-dahi babban gwamnan bankin kasar ya bayyana cewa, a cikin ‘yan shekarn nan bankin muslunci na ci gaba da kara samun bunkasa akasar.

Ya bayyana hakan ne a wani taro da ake gudanarwa a birnin Nuwakshot fadar mulkin kasar ta Mauritania, dangane da ayyukan bankuna a kasar, inda ya ce a shekara ta 2010 an samu karuwar hannayen jari da kimanin kashi 5 a bankin muslunci a kasar, amma a cikin shekarar 2016 da ta gabata, hannayen jarin bankin muslnci a kasar sun karu da kashi 14 cikin dari, kuma a cikin shhekarar da ta gabata fiye da kashi 22 na basussuka da bankunan kasar suka bayar, na bankin muslunci ne.

Daga karshe ya yi ishara da cewa, ko shakka babu ci gaba da bankin musuluncin yake samu a kasar Mauritania lamari ne mai matukar faranta rai, domin kuwa hakan zai kara bayar da dama ga masu son sayen hannyen jari a bankin daga kasashen duniya ko kuma gudanar da wasu ayyuka a karkashin bankin su saka kasar Mauritania a cikin lissafi.

3566681


captcha