IQNA

Gargadin Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama A Bahrain Ga Masarautar Kasar

21:33 - January 27, 2017
Lambar Labari: 3481175
Bangaren kasa da kasa, Kungiyoyin kare hakkin bil adama akasar Bahrain sun fitar bayani na hadin gwiwa da ke jan kunnen masarautar mulkin kama karya ta kasar kan cin zarafin al'ummar kasar da take yi musamman ma na yankin Diraz.
Gargadin Kungiyoyin Kare Hakkin Bil Adama A Bahrain Ga Masarautar Kasar
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, Shafin tashar talabijin ta almayadeen ya habarta cewa, a cikin bayanin hadin gwiwa da suka fitar yau, dukkanin kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar Bahrain sun gargadi masarautar kasar kan ci gaba da cin zarafin da take yi kan al'ummar kasar saboda dalilai na siyasa da cewa ya fara wuce gona da iri.

Bayanin ya ce ya zama wajibi masarautar Bahrain ta fahimci cewa ba za ta iya mulkar al'ummar kasar da karfin bindiga ba, domin kuwa lokacin yin mulkin kama karya da sunanan sarauta a kan al'ummar Bahrain ya wuce, kuma dole ne ta saurari kiraye-kirayen al'umma na neman a yi gyara a sha'anin mulki da kawo karshen almubazzaranci da sace kudadensu da wasu tsiraru da suke gidan sarauta suke yi.

A daren Alhamis da ta gabata ce jami'an tsaron masarautar Bahrain suka kaddamar da hari a kan gidan babban malamin addini na kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim, amma daruruwan jama'a da suke wurin sun hana su isa zuwa gare shi, duk kuwa da cewa sun yi amfani da harsasan bindiga akan jama'a, amma ala tilas sun ja da baya.

Al'ummar Baharain na zargin kasashen Amurka da Birtaniya kai tsaye a kisan gillar da masarautun Bahrain da Saudiyyah suke yi a kansu, inda suka yi gum da bakunansu, duk kuwa da karyar kare hakkin bil adama da suke yi a wasu kasashen.

3567199
captcha