IQNA

Jami'an Tsaron Kasar Myanmar Sun Kame Musulmi 32

16:54 - January 30, 2017
Lambar Labari: 3481186
Bangaren kasa da kasa, Jami'an Tsaron kasar Myanmar sun kame musulmi 23 bisa tuhumar cewa sun buga wa wasu danginsu waya da suke zaune a wajen kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron kasar ta Myanmar sun kame musulmi ne 'yan kabilar Rohingya su 32, wadanda suka tafi da wani wurin da ba a sani ba, inda suka bayar da hujjar cewa mutanen sun buga waya ne zuwa ga danginsu da suke zaune a wajen kasar.

Baya ga hakan kuma jami'an tsaron sun ce mutanen sun zauna a cikin masallaci fiye da mintuna goma bayan sallar Magariba, duk kuwa da cewa an kafa doka a kan musulmi kan su gaggauta ficewa daga cikin masallaci da zaran sun kammala sallar magariba, tare da hana su gudanar da sallar isha'i a cikin masallatai.

Makonni biyu da suka gabata ne ministocin harkokin wajen kasashen musulmi suka gudanar da zama a birnin Kualalampour na kasar Malayzia, inda suka tattauna kan halin da musulmin kasar Maynmar ke ciki, da kuma taimakon da za su iya ba su.

3568338


captcha