IQNA

An fara Gudanar Da Gasar Kur'ani A Najeriya

22:51 - February 04, 2017
Lambar Labari: 3481200
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani ta kasa baki daya a birnin Ilorin na jahar Kwara a tarayyar Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya nakalto daga shafin jaridar Tribune Online cewa, an fara gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani ta kasa baki daya a birnin Ilorin na jahar Kwara a tarayyar Najeriya da ke samun halartar wakilai daga jahohin kasa daban-daban.

Rahoton ya ce bangaren kula da harkokin nazarin addini a jamiar Dan Fodio da ke Sokoto ce ta dauki nauyin shirya wannan gasa, wadda ke samun halartar manyan jami'ai na jahar da kuma wasu sasan kasar.

Masu karatu da kuma mahardata daga jahohi 30 ne daga cikin jahohi talatin da shida da kasar take da su suka samu halartar gasar, wadda za a ci gaba da gudanarwa har zuwa mako mai zuwa.

Haka nan kuma rahoton ya yi ishara da cewa, a lokacin kammala gasar za a bayar da kyautuka na musamman ga daliban da suka fi nuna kwazo, bayan mika kyautuka na bai daya ga dukaknin wadannan suka halarci gasar.

Masu halartar wanann gasa da suka nuna kwazo ne dai suke wakiltar Najeriya a tarukan gasar kur'ani da ake gudanarwa a matsayi na duniya.

3570130


captcha