IQNA

Yara A Jahar Massachusetts Ta Amurka Sun Mika Zane-zane Nuna Kauna Ga Musulmi

22:47 - February 06, 2017
Lambar Labari: 3481204
Bangaren kasa da kasa, wasu kanan yara a jahar Massachusetts da ke kasar Amurka sun yi wasu zane-zane a kan kwalaye da takardu da ke nuna kaunarsu ga musulmi.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na bostonglobe cewa, kimanin kananan yara 150 suka gudanar da nau'in zane da ya hada da zanen zuciya da kuma kalmomi na nuna kuna da goyon baya ga msuulmi da ake ci musu zarafi a kasar.

Yaran sun yi zanen ne kuma suka saka a wani wurin shakatawa inda mutane suke taruwa, kuma ya dauki hankulan jama'a matuka.

Za a mika wadanna zane-zane ga babbar cibiyar musulmi da ke jahar a birnin Boston a ranar 14 ga wannan wata na Fabrairu a matsayin wani abu mai matukar muhimamnci ga dukkanin musulmin Amurka da ma na duniya baki daya.

Tania Nikson Silbar wadda ta shirya wannan baje kolin kayan zanen nuna kauna ga musulmi ta bayyana cewa, a kowane lokaci yara zuciyarsu tana da haske, saboda haka wajibi ne a tarbiyantar da su a kan kauna da son dan adam da kuma girmama shi.

3571111


captcha