IQNA

Azhar Da ISESCO Sun Jinjina Wa Paparoma

22:48 - February 11, 2017
Lambar Labari: 3481220
Bangaren kasa da kasa, cibiyar Azahar da kungiyar bunkasa ilimi da al;adun muslunci ta ISESCO sun jinjina wa Paparomoa Francis, dangane nuna takaicinsa da ya yi kan zaluntar musulmin Myanmar.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, cibiyar Azhar ta fitar da wani bayani wanda a cikinsa ta jinjina wa jagoran kiristoci mabiya darikar Katolika, dangane da kakkausar sukar da ya yi kan kisan gillar da ake wa muuslmi ‘yan kabilar Rohingya a kasar Myanmar.

Bangaren kula da harkokin waje na cibiyar addini ta Azhar da ke Masar ya bayyana furucin na Paparoma Francis da cewa, furuci ne na gaskiya da son adalci da kuma ‘yan adamtaka, wanda kuma wadannan suna daga cikin muhimamn abubuwan da addinan musulunci da kiristanci suke koyar da dan adama.

Shi ma a nasa bangaren Abdulazizi Al-tuwaijari babban sakataren kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adun musulunci ta kasa da kasa ISESCO, ya bayyana cewa hakika matsayar da jagoran kiristoci mabiya darikar Katolika ya dauka, matsaya ce da ta ginu a kan son adalci da kin zalunci a kan ‘yan adam.

Ya ce hakika musulmi suna farin ciki da jin hakan daga bakin Paparoma Francis, domin kuwa hakan zai kara kusanto da mabiya addinan kiristanci da muslunci tare da kara fahimtar juna da kuma zaman lafiya, domin kuwa dukkanin addinan biyu suna kiyayya da zalunci kuma kira ne zuwa sulhu da zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin dukkanin jinsi na dan adam.

Paparoma Francis ya bayyana abin da ake yin a kisan gilla a kan musulmi a kasar Myanmar da cewa aiki ne na dabbanci da zalunci, tare da yin kakakusar suka kan yadda duniya ta yi shiru ana kasha mutanen da ba su ba su gani ba, Francis ya ce duk da cewa mutanen da ake kashewa ba kiristoci ba ne, amma yana kallonsu a matsayin ‘yan uwansa, yana bakin ciki da abin da ake yi musu, kuma yana Allawadai da hakan da kakakusar murya.

3573032


captcha