IQNA

Gwamnatin Isra'ila Ta Sake Dawo Da Batun Hana Kiran Sallah A Palastine

21:43 - February 14, 2017
Lambar Labari: 3481230
Bangaren kasa da kasa, Haramtacciyar kasar Isra'ila ta sake dawo da batun hana kiran sallah a cikin wasu yankunan Palastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan kuma gabashin birnin Quds.

Kamfanin dillancin labaran IQNA ya habarta cewa, Tashar alalam ta bayar da rahoton cewa, dukkanin al'ummar palastinu suna adawa da wannan shiri na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila da ke neman a hana palastinawa yin kiran salla a cikin yankunansu.

Ahmad Mudallil daya daga cikin jagororin kungiyar Jihadul Islami ya bayyana cewa, wannan mataki yana daidai da sauran ayyukan ta'addanci na Isra'ila, kuma yana a matsayin ci gaba da take hakkokin Palastinawa da cin zarafinsu da kuma keta alfarmar addininsu da Isra'ila ke yi a tsawon tarihinta.

Ahmad Abu Haliba shugaban cibiyar Al-quds ya bayyana cewa, a'ummar Palastinu ba ta taba amincewa da wannan sabuwar doka ta zalunci da Isra'ila ke neman kafawa a kansu ba, domin kuwa kiran salla wani bangare na addini, da ba za a raba al'ummar musulmi na palastinu da shi ba.

Tun a cikin shekarar da ta gabata ce haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara batun hana Palastinawa yin kiran sallah, amma batun ya fuskanci tsaiko daga majalisa, inda a halin yanzu gwamnatin Netanyahu ta sake shirya wani sabon daftarin kudiri a kan wannan batu.

3574503


captcha