IQNA

An Gudanar Da Taro Kan Kur'ani A Jami'ar Oklahoma

20:54 - February 18, 2017
Lambar Labari: 3481242
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani zaman taro domin bayani kan wasu batutuwa 10 a cikin kur'ani da ake yi ma muslunci mummunar fahimta a kansu wato jihadi da kuma hakkokin mata a muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin OUDaily cewa, Imad Insha'i babban limamin masallacin birnin Oklahoma ya gabatar da jawabi a wurin taron.

A cikin jawabin nasa ya yi ishara da cewa, akwai batutuwa da ake yawan yin amfani da su domin sukar muslunci ko kuma bata masa suna, daga ciki kuwa har da batun jihadi da kuma hakkokin mata a cikin addinin musulunci.

Ya ce ko shakka babu musulunci baya amfani da jihadi a matsayin wani makami na danne wasu kabilu ko al'ummomi ko kuma wasu addinai, jihadi yana a matsayin wata hanya ce ta kare kai a muslunci daga masu yin shishii a kan musulmi, ko kuma wasu da suke cutar da musulmi.

Domin kuwa za a ga cewa manzon Allah ya zauna mabiya addinai daban-dabana birnin madina ba tare da wani ya tilasta su su shiga musulunci ba, kuma babu wanda ya cutar da su, domin kuwa muslunci bai zo domin tilasci, daya daga cikin kaidojin da kur'ani ya koyar da musulmi ma ita ce; babu tilascia cikin addini, kur'ani ya ambaci haka karara.

A bangare hakkokin mata kuwa, muslunci yana kare hakkin mace a dukkanin bangarori na rayuwa, wanda wata kila hakan ne ma ya sanya wasu suke kallon musulunci kamar yana take hakkokin mata domin ya sanya su saka sutura da za ta rufe jikinsu, wanda hakan idan aka yi la'akari shi ne babban abin da yake baiwa mata aminci a cikin al'umma.

Amam a idan aka duba sauran bangarori muslucni y aba mata dama su shiga cikin fagage na ilimi su yi karatu mai zurfi kamar maza, su taimaka ma al'umma, su ilmantar da al'umma su tarbiyantar da ita bisa sahihiyar tarbiya a rayuwa, saboda haka muslucni yana kallon mace a matsatin mutum mai cikakkiyar kima da daraja da matsayi na musamman a cikin al'umma da rayuwa ta zamantakewa.

3575418


captcha