IQNA

Shirin Taimakon Masu Cutar Cancer GIdan Radiyon Kur'ani Na Nablus

21:48 - February 20, 2017
Lambar Labari: 3481247
angaren kasa da kasa, gidan radiyon kur'ani da ke birnin Nablus a Palastine ya bullo da wani shiri domin taimaka masu fama da cutar cancer.

BKamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin Dunya Alwatan cewa, gidan radiyon kur'ani ya fara gudanar da wani shiri na musamman dangane da yadda mutane za su taimaka masu fama da matsalar cancer wato ciwon daji

Wannan shiri dai za a gudanar ad shi ne tare da hadin gwaiwa da ma'aikatar kula da harkokin lafiya ta kwarya-kwaryan cin gishin kai ta Palastine, tare da taimakon wasu daga cikin masu hannu da shuni.

Daga cikin abin da shirin zai mayar da hankali a kansa akwai wayar da kan jama'a jama'a kan abubuwan da ya kamata su rika yi domin taimakon masu fama da wannan cuta, kamar yadda kuma za a rika zantawa da likitoci domin wayar da kan kan hanyoyin da ya kama abi domin kaice ma kamuwa da ita.

Shirin dai yana zuwa ne la'akari da karuwar masu kamuwa da wannan cuta ne a cikin yankunan Palastinawa, sakamakon matsaloli da dama da suke fama da sun a karancin magunguna sakamakon takunkumin zalunci da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kafa musu.

Bayan nan kuma akwai hanyar yin amfani da kwantarwa mai fama da wanann matsala hankali, daga cikin irin wadannan hanyoyi kuwa har sanya shi ya rika saurare wasu daga cikin ayoyin kur'ani mai tsarki.

Al'ummomi da dama a yankunan Palastinawa sun nuna jin dadinsu da kuma gamsuwarsu da hakan, tare da yin kira ga gwamnatin cin gishin kai ta Palastinawa da ta tallafawa wanann shiri domin ya yi nasara.

3576415


captcha