IQNA

An Shiga Mataki Na Karshe Na Gasar Kur'ani Ta Makafi A Oman

22:47 - February 22, 2017
Lambar Labari: 3481253
Bangaren kasa da kasa, an shiga mataki na karshe a gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta makafi a kasar Oman.

BKamfanin dillancin labaran kur'ani na IQNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin jaridar Oman cewa, a yau ne aka shiga mataki na karshe a gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta makafi a kasar Oman

Wannan gasar dai ana gudanar da ita ne a kowace shekara, inda daga ann za a zabi wadanda za su je gasar tantance wadanda za su wakilci kasara gasar kur'ani ta duniya ta nakasassu.

Ma'aikatar ilimi ta kasar Oman tana bayar da muhimmanci matuka ga karatun masu nakasa a kasar, da hakan ya hada da bangaren karatun boko da kuma na addini, musamman a bangaren koyon karatun kur'ani mai tsarki.

Cibiyar kur'ani ta Umar Bin Khattab da ke kasar ta Oman ce dai take daukar nauyin shirya irin wannan gasa tare da taimakon ma'aikatar kula da harkokin ilimi ta kasa.

Bayanin ya ce za a bayar da kyautuka na musamman ga dukkanin wadanda suka shiga cikin gasar, kamar yadda kuma za a bayar da wasu kyautukan ga wadanda suka fi nuna kwazoa gasar, wadanda daga cikinsu ne za a dauki wadanda za su wakilci kasar a gasar kur'ani ta nakasassu ta duniya.

3577105


captcha