Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin jaridar Mir'ar Bahrain ya bayar da rahoton cewa, kotun masarautar kasar ta Bahrain ta sanar da cewa, ta dage zaman yanke hukunci a kan Sheikh Kasim zuwa ranar 14 ga watan maris mai kamawa.
Kafin wannan lokacin da alkalin alkalan masarautar Bahrain, ya sheda cewa za a yanke hukunci na karshe a kan sheikh Isa Kasim.
Gidan sarautar bahrain na zargin Sheikh Ayatollah Isa Kasim da goyon bayan 'yan adawar siyasa a kaar, wadanda suke nuna rashin gamsuwarsu da salon mulkin masarautar kasar.
A kan wannan dalili masarautar ta sanar da janye izinin zama dan kasa a kan malamin, wanda shi ne ya fi kowa yawan mabiya a kasar, tare da bayar da umarnin a fitar da shi daga daga lasar, amma hakan ta faskara, domin kuwa al'ummar kasar Bahrain sun sha alwashin kare rayuwar shehin malamin har zuwa karshen lumfashinsu.