IQNA

Daurin Shekaru 5 A Kan Wani Malamin Masar Bisa Zargin Tozarta Muslunci

23:08 - February 28, 2017
Lambar Labari: 3481271
Bangaren kasa da kasa, Wata kotu a kasar masar ta zartar hukuncin daurin shekaru 5 a gidan kaso a kan wani malmin addini mai suna Muhammad Abdullah da aka fi sani da sheikh Mizo, bisa zarginsa da tozarta ababe masu tsarki a muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin yada labarai na Alhurra ya bayar da rahoton cewa, kotun birnin Shibra Alkhaima da ke cikin gundumar Kailubiyya ta yanke hukuncin daurin shekaru 5 a gidan kaso a kan sheikh Mizo, bayan da ya nuna rashin amincewarsa da wasu daga cikin hadisan manzo ingantattu a wajen ahlu sunna, inda kotun ta ce hakan yana a matsayin tozarta hadisan manzo ne.

Jim kadan bayan yanke hukuncin, kotun ta bayar da umanin a tsare sheikh Mizo a gidan kason Shibra Alkhaimah, domin ya yi zaman kaso a wurin, amma bayan sanar da hukuncin daurin shekaru 5 a kansa, sheikh Mizo ya fara yajin cin abinci.

A kwanakin bayan ne malamin ya ce shi ne Mahdi da aka yi alkawalin zai bayyana a karshen duniya, kuma yana kiran dukkanin musulmi sunnah da shi'a da su yi masa mubaya'a, furucin da ya fusata da dama daga cikin malaman addini a kasar Masar.

3578826


captcha