IQNA

Mutane 700 Da Ba Musulmi Ba Sun Halarci Masallacin Carolina

20:31 - March 12, 2017
Lambar Labari: 3481306
Bnagaren kasa da kasa, a wani shiri da musulmin jahar Carolina ta arewa a kasar Amurka suke gudanarwa kimanin mutane 700 da ba musulmi ba ne suka halarci wurin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na «wncn» cewa, an gudanar da wani shiri a cikin Carolina da ke kasar Amurka na kara fahimtar da mutanen da ba musulmi mene ne addinin muslunci.

Kimanin mutane 700 wadanda ba musulmi ba sun halarci masallacin birnin Rally, shirin mai taken kofofin masallaci a bude, na nufin bayar da dama ga duk mai son ya zo masallaci ya ga yadda musulmi suke gudanar da ibada, kuma ya tambaye su abin da ya shige masa duhu dangane da muslunci.

Daruruwan mutanen da suka e wurin sun ga yadda muslmi suke yin salla da addu’oi, bayan nan kuma an gabatar da jawabi a gare su kan addinin muslunci na hakika, sabanin yadda ake ta kokarin bayyana wanann addini a idon duniya.

Babbar manufar shirin dai ita ce kalu balantar sabon shirin gwamnatin Amurka ta yanzu, wadda ta shelanta kyamar musulmi a hukumance, tare da daukar matakan bayar da cikakken goyon baya ga duk wani mai adawa da musulmi a kasar.

Da dama daga cikin wadanda suka halarci irin wannan shiri da msuulmi suke gudanarwa a masallatai a kasar ta Amurka, suna samun canjin tunani dangane da addinin muslunci.

3583203

captcha