IQNA

Shugaban India Ya Aike Da Sakon Murnar Shiga Sabuwar Shekarar Hijira Shamsiyyah

22:37 - March 21, 2017
Lambar Labari: 3481332
Bangaren kasa da kasa, Shugaban kasar India Pranab Mukherjee ya aike da sakon taya murnar shiga sabuwar shekara ta hijira shamsiyyah ga al'ummar Iran baki daya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, cikin sakon da ya aike wa shugaba Hassan Rauhani na kasar Iran a yau, shugaban kasar India Pranab Mukherjee ya bayyana cewa, yana taya daukacin al'ummar kasar ta Iran murnar shiga sabuwar shekara ta hijira shamsiyyah, tare yin fatan samun alkhari da albarka da zaman lafiya a cikin wanann shekara ga dukaknin al'ummomi na duniya.

Shugaban na India ya bayayan shekarar hijira shamsiyya a matsyin lamari mai tsawon tarihi wanda ya hada al'ummomi da dama tun fiye da shekaru dubu biyu da suka gabata, wanda kuma al'ummomin Iran da India suna daga cikin al'ummomi masu dadadden tarihi na alaka tun fiye da shekaru dubu biyu.

Shekarar hijira shamsiyya ta fara ne tun fiye da shekaru dubu dubu da dari biyar da suka gabata, duk kuwa da cewa an daidaita ta da hijira ta muslunci bayan zuwan addinin muslunci a cikin kasashen farisa.

3585373

captcha