IQNA

Tattaunawa Tsakanin Addinin Muslunci Da Kiristanci A Scotland

22:07 - March 25, 2017
Lambar Labari: 3481346
Bangaren kasa da kasa, ana shirin gudanar da wani shiri na musamman kan tattaunawa tsakanin mabiya addinin kiristanci da muslunci a Scotland.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, «shetnews» cewa, za a gudanar da wannan shiri da nufin kara kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiyan addinai kiristanci da kuma muslunci, inda FananaPazir wata likitan zuciya daga Miriland ta Amurka za ta gabatar da jawabi a wurin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake gudanar da irin wannan taro a Scotland ba, domin kuwa yankin na daga cikin yankuna da musulmi suke gudnar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali

A shekarar da ta gabata an gudanar da wani taro mai kama da wannan inda aka gudanar da tattaunawa tsakanin mabiya addinai na Buda da kuma kiristanci.

Yanzu haka dai akwai musulmi fiye da dubu 50 a cikin Scotland, baya ga haka kuma suna da masallatai kimanin 30 wadada ake gudaar da dukkanin sallo a cikin a kowace rana.

3585641

captcha