IQNA

Mahangar Kur'ani A Kan Jahilci Da Jahilai

17:01 - September 03, 2017
Lambar Labari: 3481859
Bangaren kasa da kasa, wani mai bincike kan ilimin kur'ani ya gabatar da rubutunsa na karshe kan bincike dangane ma tsayin kur'ani a kan jahilci da kuma jahilai.
Kamfanin dillancin labaran iqna yahabrata cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na sadal balad cewa, Abdulhay Anwar Isma'il wani mai bincike kan ilimin kur'ani dan kasar Masar ya rubuta littafi kan bahasi dangane da matsayin jahilci da kuma jahilai a mahangar kur'ani.

A cikin rubutun nasa, ya bayyana yadda kur'ani yake bayyana jahilci wato abin da ake kira da jahilci ko kuma abubuwan ad su ne jahilci, da kuma jahilai mutanen da ake kira jahilai da abin da yasa ake kiransu da wannan siffa wadda ta damfara su da jahilci.

Marubucin yace akwai wasu abubuwa wadanda kan yi tasiri a cikin lamarin jama'a da rayuwarsu ta zamantakewa, wata kila sun tashi ne a cikin wanann yanayi da suka gada daga iyaye da kakanni, ko kuma sabbin abubuwa ne suka shigoa cikin al'ummma kuma suka yi tasiri.

Bisa ga dabia ta larabawa, sukan mayar da kansu jahilai wajen bin salon da ska gada daga iyaye da kakanni ko da kuwa daga bisani sun fahimci jahilcin magabantansu, wanda hakan yana daga cikin abin da kur'ani ya zargi larabawan jahiliyya da shi.

Kamar yadda kuam rashin yin aiki da ilimi yana matsayin jahilci amma kuma a lokaci guda shi yafi jahilci muni, domin shi yana hade da sani amma kuma aka bijire.

3637626


captcha