IQNA

Jagora Ya Yi Addu'a Ga Shahid Hujaji A safiyar Yau

16:21 - September 27, 2017
Lambar Labari: 3481938
Bangaren siyasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatollah Sayyid Khamenei ya bayyana shaheed Muhsen Hujaji wanda ya yi shahada a hannun mayakan Daesh a kasar Siriya yana da matsayi na musamman a zukatan mutanen Iran, All.. ya daukaka shi a cikin shahidai masu kare harami
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Jagoran ya bayyana haka ne safiyar yau Laraba a lokacinda ya je kusa da gawar shahid Muhsen Hujaji wanda aka ajiye a masallacin Imam Husain (a) da ke cikin birnin Tehran. Jagoran ya kara da cewa, shahidai gaba daya suna da babban matsayin a wajen Allah amma wasun Allah ta'ala yakan daukakasu akan wasu. Kamar dai yadda muke ganin yadda wannan shihidin ya shiga cikin zukatan ummar kasar Iran.

A yau Laraba ce za'a zagaya da gawar Shahid Muhsen Hujaji daga Masallacin Imam Husain (a) da ke nan Tehran zuwa dandalin shaheed duk a nan cikin Tehran

Shahid Hujaji ya yi shahada ne a ranar 9 ga watan Agustan da ya gabata a lokacin da mayakan Daesh suka kama shi a kan iyakar kasar Syria da Iraqi a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa hariman Sayyida Zainab dake birnin Demascus na kasar Syria.

3647030


captcha