IQNA

An Gano Wasu Makaman Roka 160 A Karbala

23:14 - September 30, 2017
Lambar Labari: 3481950
Bagaren kasa da kasa, jami'an tsaro sun gano wani shirin kai harin bam a birnin Karbala a lokacin da ake traukar tasu'a.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da da rahoton cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar al'alam cewa, a daidai lokacin da ake traukar tasu'a jami'an tsaro sun gano wani shirin kai harin bam a birnin Karbala.

Tun kafin wannan lokacin dai an kama mutane masu yunkurin kaddamar da hare-haren ta'addanci a birnin na Karbala da kuma wasu yankuna na kasar Iraki.

Ko a cikin makon da ya gabata ma an kame wasu 'yan ta'addana lokacin da suke shirin kaddamar da wasu hare-hare makamantan hakan.

A yau ne ake gudanar da tarukan tasu'a a dukkanin yankuna na kasashen duniya, domin nuna juyayi kan abubuwan da suyka wakana a wannan lokaci na shahadar iyalan gidan manzo.

Wannan mataki da jami'an tsaron Iraki suka dauka, ya hada dukaknin birane da yankuna na kasar da ake gudaar da irin wadannan taruka ne, da hakan ya hada bababn birnin kasar da kuma sauran birane inda ke da hubbarori masu tsarki.

3647825


captcha