IQNA

Ayyana Quds A Matsayin Birnin Isra’ila Masomi Ne Na Shiga Wani Sabon Yanayi

23:00 - December 07, 2017
Lambar Labari: 3482177
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana matakin da shugaban Amurka ya dauka kan mayar da birnin Quds fadar Isra’ila da cewa masmi ne na shiga wani yanayi.

Ayyana Quds A Matsayin Birnin Isra’ila Masomi Ne Na Shiga Wani Sabon YanayiKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Babban sakataren kungiyar Hezbollah ta kasar Labanon, ya mayar da martani dangane da matakin Donald Trump na ayyana birnin Qudus a matsayin babban birnin HK Israila.

Da yake gabatar da jawabinsa a gidan talabijin, Sayyid Hassan Nasrallah, ya ce a game da wannan matakin, mahukuntan yahudawan sahayoniya zasu ci gaba da mamaye Palastinu da zalintar al'ummarta ta hanyar kwace masu filaye da gidaje.

A yayin da yake ishara kan cewa masallacin Qudus shi ne tushen mas'alar Palastinu, sayyid Nasrullah ya tabbatar da cewa wannan mataki da Trump ya dauka cin mutunci ga milyoyin al'ummar musulmi, da kirista, saboda garin Qudus, gari ne dake da wurare masu tsarki da tarihi na wadannan al'ummomi.

Sayyid Nasrullah ya kuma ce, shirun duniyar musulmi na kara raunana al'ummar Palastinu da kuma kara karfin makiya akan wasu wurare masu tsarki na musulmi.

Wasu na ganin cewa wannan matakin da Trump ya dauka, kawo karshen tattauanawar zaman lafiya ne tsakanin hukumomin HKI da na Palastinu, wasu kuma na ganin cewa tun a baya batun tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin biyu ya kawo karshe.

A hannu daya kuma babban sakataren kungiyar ta Hezbollah, Sayyid Nasrollah, ya ce wannan matakin na Trump ya nuna yadda bai mutunta dokokin kasa da kasa, hatta ma kasashe kawayen kasarsa Amurka, da jami'an gwamnatinsa, kawai babban abunda yake gabansa shi ne kare manufofin Isra'ila.

Sayyid Hasan Nasrullah ya ce wajibi ne kasashen larabawa da na musulmi su kira jakadan Amurka dake zaune a kasashensu su kuma bayyana masa rashin yardar su da wannan mataki.

3670476

 

captcha