IQNA

Azhar Ta Mayar Da Martani Kan Murkuse Intifadar Palastinawa

23:34 - December 16, 2017
Lambar Labari: 3482207
Bangaren kasa da kasa, Kwamitin manyan malaman jami'ar Azhar ta Masar ya bukaci tallafawa al'ummar Palasdinu da kudade domin samun damar ci gaba da gudanar da boren da suke yi na kare birnin Qudus.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Kwamitin manyan malamai na Jami'ar Azhar da ke kasar Masar a jiya Talata ya fitar da bayanin cewa: Akwai bukatar tallafa wa al'ummar Palasdinu da kudade domin ci gaba da gudanar da boren da suke yi na kare Masallacin Qudus tare da birnin daga mamayar Yahudawan Sahayoniyya.

Kwamitin manyan malaman na jami'ar Azhar ya gudanar da zaman taron gaggawa ne da nufin tattauna hanyoyin da suka dace a bi domin kalubalantar matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila tare da bada umurnin maida ofishin jakadancin kasar ta Amurka zuwa birnin Qudus.

Tun kafin wannan lokacin dai Azhar ta bayyana matsayarta dangae da batun kudirin na Trump da cewa ba abu ne da za a lamunta shi ba.

Daga cikin matakan da cibyar ta dauka har da yin watsi da wan shirin ganawa tsakanin mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka da kuma baban malamin cibiyar da aka shirya gudanar.

 

3672924

 

 

captcha