Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na bangaren hulda da jama'a na cibiyar yada al'adun muslunci cewa,tawagar Mi'ad daga yankin Ahwaz ta halarci wani taron kur'ani da aka shirya a Senegal.
Wannan taron dai an shirya shi ne domin gabatar da karatun kur'ani da wakokin bege ga manzon Allah wanda, wanda cibiyar Nabiyullah ta shirya, kuma ta gayyaci kungiyar Mi'ad daga Iran.
Taron dai an gudanar da shia daren jiya, tare da halartar malamai da kuma masana, gami da makaranta kur'ani, kamar yadda kuma wasu daga cikin larabawa mazauna birnin Dakar suka halrci gami da jami'ar Almustafa (SAW) a reshenta da ke kasar ta Senegal.
Taron dai ya samu karbuwa daga mutane da daman a kasar Senegal.