IQNA

Taron Nuna Kin Aincewa Da Matsayar Trum Kan Quds A Zimbabwe

23:59 - December 18, 2017
Lambar Labari: 3482213
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zama na nuna kin rashin amincewa da matsayar Trump na Amurka kan birnin Quds a Zimbabwe.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya an gudanar da zama na nuna kin rashin amincewa da matsayar Trump na Amurka kan birnin Quds a Zimbabwe wanda ya hada musulmi da mabiya addinin kirista.

Sheikh Abdullan Mangija shi ne shugabab cibiyar Zahra (AS) ya bayyana cewa manufar taron it ace tabbatarwa duniya da cewa dukaknin addininai bas u amince da wannan matasaya ta Donald Trump kan birnin Quds mai alfarma ba.

A kasar Amurka ma dubban musulmi a kasar sun gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da matakin da shugaban kasar Donald Trump ya dauka na shelanta birnin Qudus a matsayin fadar mulkin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila.

Majalisar Musulmin kasar ta Council of Muslim Organization ce ta shirya zanga-zangar, inda dubban al'ummar musulmin Amurka da kungiyoyin musulmi fiye da talatin da biyar  suka halacci zanga-zangar suna rera taken jaddada goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu da ake zalunta tare da daga kwalaye da suke dauke da rubuce-rubucen cewa: Trump da Natenyahu suna son kunna wutan yaki, Birnin Qudus fadar mulkin al'ummar Palasdinu ne da sauransu.

Masu zanga-zangar sun tafi har zuwa Majalisar Dokokin Kasar Amurka suna bayyana goyon bayansu ga al'ummar Palasdinu tare da neman mahukuntan kasar da su hanzarta janyewa daga mummunan matakin da shugaban kasar Donald Trump ya dauka kan birnin Qudus domin warware rikicin Palasdinawa da Yahudawa cikin adalci.

Tun a ranar shida  ga wannan wata na Disamba ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauki matakin shelanta birnin Qudus na Palasdinu a matsayin fadar mulkin gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila tare da bada umurnin maida ofishin jakadancin Amurka daga Tel-Aviv zuwa birnin na Qudus lamarin da ya ke ci gaba da fuskantar tofin Allah tsine daga sassa daban daban na duniya.

3673744

 

 

captcha