IQNA

Masar Za Ta Dauki Bakunci Taron Fada Da Tsattsauran Ra’ayin Addini

21:01 - December 21, 2017
Lambar Labari: 3482222
Bangaren kasa da kasa, kasar Masar za ta dauki bakuncin taro ma taken fada da tunanin tsatsauran ra’ayin addini a birnin Iskandariyya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Bawaba News cewa, cibiyar yada al’adu da ilimi ta kasashen musulmi wato ISESCO ita ce ta dauki nauyin shirya gudanar da wannan zaman taro.

Babbar manufar shirya gudanar da taro a wata mai zuwa ita e, sama da hanyoyi na kalu balantar duk wani tunani na tsatsauran ra’ayi a cikin musulmi, tare da fito da sabbin hanyoyi na gudanar da wannan garumin aki, musamman ta hanyoyi na yanar gizo da kuma shafukan yada zumunta da sauransu.

Malami da masana da za su halarci taron za su gabatar da kasidunsu wadanda suke dauke da maudu’ai daban-daban dangane da manufar gudanar da taron da kuma abin ya kunsa.

Baya ga haka kuma akwai batun gyara kayan tarihi da mayakan ‘yan ta’addan wahabiyawa suka lalata a kasashen Syria, Iraki, Ymen da kuma Afghanistan, wanda hakan yake bukatar hadin gwiwa da haduwar mahana da ra’ayoyi na masana.

3674796

 

 

 

 

 

captcha