IQNA

Gasar Kur'ani Mai Taken Quds A Kasar Masar

23:46 - December 25, 2017
Lambar Labari: 3482234
Bangaren kasa da kasa, nan da watanni masu zuwa za a gudanar da wata gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa  akasar Masar wadda aka yi wa take da Quds ta larabawa ce.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na Egypt Today cewa, za a gudanar da wata gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa karo na ashirin da biyar a kasar Masar wadda aka yi wa take da Quds ta larabawa ce, taken da ke a matsayin martini ga matakin Amurka kan batun birnin Quds mai alfarma.

Bayanin ya ci gab ada cewa wannan gasa za ta kasance kamar yadda aka saba gudanarwa, inda akan kasa bangarorin gasar zuwa harda da kuma karatu, tare da halartar kasashen duniya.

Daga cikin bangarorin da gasar za ta tabo a wannan karo bayan harda da kuma karatun tilawa, akwai bangaren hukuncehukunce na karatun kur'ani, sai kuma bangarori na fikihu da tafsiri da sauransu.

Masu gasa 60 ne dai za su shiga wannan gasa a wannan karo, 43 daga cikinsu dai 'yan kasashen ketare ne, da suka fito daga Afghanistan, Kamaru, Afirka ta tsakiya, Algeria, Morocco, Nigeria, Masar, Komoro, Burkina Faso, Palastine, Saudiyya, Baharain, Senegal, Sudan, Kirgistan, Oman, Jordan, Canada, Amurka, Australia, Jordan, Ivory Coast, Maldev, makdonia, Rasha, India, Azarbaijna, Uganda, Faransa, Myanmar da Singapore.

3675620

 

 

 

 

captcha