IQNA

An Tarjama Kur’ani A Cikin Harshen Mutanen Burundi

23:46 - December 26, 2017
Lambar Labari: 3482237
Bangaren kasa da kasa, a karon farko an tarjama kur’ani mai tsarki a cikin harshen mutanen Burundi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sheikh Sadiq Kujandi shugaban majalisar muuslmin Burndi ya bayyana cewa, wannan shi nr karon farko da aka tarjama kur’ani mai tsarki a cikin harshen mutanen kasar.

Ya ci gaba da cewa, wannan babban abin farin ciki ne ga dukkanin muuslmi na wannan yanki, domin kuwa bayan kwashe sekaru 8 a jere ana wannan aikin tarjama, yanzu an kammala.

Ana magana da harshen Rwandi a  kasashen Burundi, da wasu yankuna na Tanzania, jamhuriyar dimukradiyyar Congo da kuma Uganda.

Musulmi su ne kashi 10 cikin dari na utane miliyan 11 da e rayuwa  akasar Burundi, kuma suna rayuwa e a biranen Gitga, Romunko da kuma Bujumbura fadar mulkin kasar.

Musulunci ya isa Burundi ne a cikin karni na sha tara.

3676652

 

 

 

 

 

 

 

captcha