IQNA

Rawar Da Musulmi Suka Takawa A Trinidad and Tobago

23:08 - May 03, 2018
Lambar Labari: 3482627
Bangaren kasa da kasa, musulmi suna taka gagarumar rawa kasar Trinidad and Tobago.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yanar gizo na sadal balad cewa, duk da cewa adadin musulmi a kasar Trinidad and Tobago bai kasha 8 cikin dari ba, amma duk da haka suna taka gagarumar rawa ta fuskar siyasa da zamantakewa da kuma tattalin arzikin kasar.

Musulmin kasar sun iya gina masallatai 115, kamar yadda kuma suka gina cibiyoyin addini da suke hade da makarantu guda 14

Akasarin musulmin wannan kasa dai Indiyawa ne da suka yi hijira da jimawa, kuma gwamnatin kasar ta gimama musulmi da addinin muslunci, inda ake bayar da muhimmanci ga wasu ranaku na musamman na musulmi musamman a watan Ramadan, baya ga haka kuma hutu ne a hukumance a ranar karamar salla.

Kasar Trinidad and Tobago dai tana a yankin latin Amurka ne, kuma ta kasance karkashin mulkin mallaka na turawan Birtaniya,a  cikin shekara ta 1962 ta samu ‘yancin kanta.

3711108

 

 

 

 

 

 

captcha