IQNA

An Bude Taron Tattaunawa Tsakanin Addinai A Kasar Tunusia

23:49 - May 04, 2018
Lambar Labari: 3482631
Bangaren kasa da kasa, an bude zaman taron tattaunawa tsakanin mabiya addinai da aka saukar daga sama a kasar Tunusia a garin Jarba domin yaki da akidar ta'addanci.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na alarabi jaded ya habarta cewa, an bude zaman taron ne tare da halartar manyan malaman addinin muslunci da kuma malaman yahudawa da kiristoci.

Yusuf Shahed firayi ministan kasar Tunusia, a lokacin da yake gabatar da jawabin bude taron ya bayyana cewa, ko shakka babu addinin muslunci yana yin kira zuwa ga zaman lafiya da fahimtar juna tsakaninsa da dukkanin sauran addinai, musamman wadanda ak asaukar daga sama.

Ya ce kamar yadda addinin muslunci yake haka sauran addinai da aka saukar daga sama suke, babu wani addini na Allah da yake kira zuwa ga ta'addanci ko kisan jama'a ba gaira ba sabar, kamar yadda kuma dukkanin wadannan addinai suna kira zuwa fahimtar juna da grmama dana dam.

Ya ce ana samun masu tsatsauran ra'ayi da suke wuce gona da iri a cikin wadannan addinai, kamar yadda ake samunsu a cikin musulmi, haka ake samunsua  cikin yahudawa da kiristoci, amma kuma abin da suke yi ba suna wakilatar wadannn addinai ba ne.

Sheikh Usman Battikh babban malamin addini na kasar Tunusia ya halarci, inda shi ma ya gabatar da nasa bayanin kan uhimmancin fahimtar juna tsakanin mabiya addinai da kuma zaman lafiya.

3711263

 

captcha