IQNA

Oman Ta Sanar Da Ranar 17 Ga Watan Mayu A Matsayin Ranar Farko Ta Ramadan

23:48 - May 07, 2018
Lambar Labari: 3482638
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Oman ta sanar da ranar 17 ga watan Mayu a matsayin ranar farko ta watan ranadan mai alfarma na wannan shekara.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, shafin yada labarai na jaridar K Times ta ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Oman ta fitar ta bayyana cewa, ba zai yiwu a ga wata a daren Talata ba 15 ga watan Mayu, saboda haka ranar Alhamis ce daya ga watan Ramadan.

Ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Oman ta yi fatan alhairi ga dukkanin musulmi na duniya baki daya da fatan samun dacewa a cikin a cikin wannan wata na Ramadan mai kamawa.

Wasu daga cikin kasashen musulmi dai har yanzu su a bin lissafin wata ne kafin bayyana matsayarsu kan watan mai kamawa.

3712064

 

 

captcha