Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar sojin Iran Yahya Rasul ya sanar da cewa, sun fara kaddamar da farmakin ne a yankunan Pishgan da Tal Zahab a cikin lardin Samirra.
Ya ce sun samu nasarar rusa wasu muhimman wuraren buyar ‘yan ta’adda guda biyu da suke a wurin, kuma an kashe daya daga cikin ‘yan ta’addan, yayin sauran kuma suka mika kansu.
Wannan farmaki dai ya zo ne sakamakon hare-haren baya-bayan nan da ‘yan ta’addan Daesh suka kaddamar a wasu yankuna na Iraki, kamar yadda kuma ake zaton cewa ‘yan ta’addan za su zafafa hare-harensu a cikin ‘yan kwanakin nan domin kawo cikas ga zaben da za a gudanar a kasar.