Kamfanin dillancin labaran iqn ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ufuq News cewa, a yau an gudanar da bikin girmama mahardata kur’ani 370 a lardin Shubwa na Yemen da suka hada da maza da mata, tare da halartar Ahmad Zabin bin Atiyah ministan harkokin addini na kasar.
Haka nan kuma Ali Bin Salem Alharisi gwamnan Lardin Shubawa shi ma ya samu halartar wurin.