IQNA

Akwai Yiwuwar A Sake Kai harin Ta'addanci Kan Musulmi A Afirka Ta Kudu

23:51 - May 14, 2018
Lambar Labari: 3482658
Bangaren kasa da kasa, akwai yiwuwar a sake kaddamar da harin ta'addanci kan msuulmi a kan masallatan a Afirka ta kudu.

 

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran reuters cewa, jami'an 'yan sanda sun samu wani buhu da aka ajiye a kusa da wani masallaci a garin Durban na Afirka ta kudu, wanda ake zaton cewa bam ne.

Jami'an tsaron sun ce an bukaci jama'a da su kaurace wa wurin domin masana kan harkokin abubuwan masu fashewa su gudaar da bincike.

Wannan dais hi ne karon farko da aka kaddamar da farmaki a kan masallacin mabiya mazhabar shi'a  akasar Afirka ta kudu, duk da cewa dai har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin hakan, amma dai ana nuna yatsun tuhuma  akan kungiyoyin wahabiyawa masu masu tsatsauran ra'ayi.

A ranar Alhamis da ta gabata ce wasu mutane uku suka kutsa kai cikin masallacin, inda suka yi ta daba ma mutane wuka, sun kasha mutum daya sun kua jikkata wasu biyu.

3714195

 

 

 

 

captcha