IQNA

Ana Shirin Fara Gudanar Da Babbar Gasar Kur’ani Ta Azhar

23:50 - May 16, 2018
Lambar Labari: 3482664
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da gasar nan ta sekara-shekara ta Azhar domin fita da gogaggun makaranta.

 

Kamfanin dillancin labaran ina ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yaum sabe cewa, an kammala dukkanin shirin fara gudanar da gasar kur’ani ta Azhar.

A yayin wannan gasar ne ae fitar da ggaggun makaranta kur’ani wadanda za s rika wakiltar cibiyar a harkokin da suka shafi kur’ani da gasa da kuma tarukan da ake bukatar makaranta domin bude manyan taruka.

Baya ga haka kuma ana fitar da wadanda za su kasance su ne makaranta a hukumance, kama daga gidajen talabijin da radiy na gwamnati da sauran dukkanin abubuwan da ake bukatar makaranta daga cibiyar Azhar.

Yanzu haka an kammala karbar sunayen dukkanin wadanda suka rijistar shiga cikin shirin, wanda za a fara a cikin wannan wata ramadana mai alfarma.

Wani jami’in cibiyar ta azhar ya bayyana cewa daga cikin wadanda za su shiga shirin har da wasu daga wajen jami’ar.

3715207

 

 

 

 

captcha